1. Ka Rage Magana:
Yawan magana ba alamar wayo ba ce. Halittar ɗan Adam ta zo da kunne biyu da baki ɗaya – domin a fi sauraro fiye da magana.
2. Ka Koyi Faɗin "A'a":
Kar ka dinga amincewa da abubuwan da zasu cutar da kai kawai don ka faranta. Alkawarin da ya fi ƙarfin ka yana kawo saɓani da raini.
3. Kada Ka Yiwa Tambaya Amsa Da Gaggawa:
Idan aka tambaye ka, kayi shiru ɗan lokaci – kayi tunani kafin ka bada amsa. Maganar da ta fita ba zata dawo ba.
4. Yi Tunani Kafin Yanke Hukunci:
Gaggawa aikin shaidan ne. Wanda ya yi garaje yafi saurin tuntuɓe da nadama.
5. Ka Rage Yawan Nunawa Kanka:
Kar kowa ya dinga ganinka sai dai a wuraren da suka dace kamar wajen aiki. Abinda yafi yawa yana rasa kima. Daraja na buƙatar sirri da natsuwa.
6. Ka Guji Gardama Da Kowa:
Musamman da abokai ko iyali. Yawan gardama yana nuna ƙarancin hankali da rainin wayo. Yana iya kawo kiyayya da rashin daraja.
7. Kullum Ka Saka Tufafin Tsabta:
Ko da tsofaffi ne, ka tabbatar kana tsaftace su. Kamala a sutura na nuni da mutunci da ɗaukaka.
8. Ka Kula Da Maganganun Ka:
Kada ka dinga saka baki a dukkan magana, ko da an tambaye ka. Karya da zagi suna rage mutumci. Harshenka yafi kaifi fiye da takobi.
9. Ka Ƙware a Wata Sana’a:
Kada ka dogara da roƙo. Sana’a na kawo girma. Wanda ke neman halal baya buƙatar ƙasƙantar da kai a gaban wani.
10. Guji Maye da Duk Wani Abu Mai Gusar da Hankali:
Shan kayan maye yana lalata lafiya da mutunci. Ba ya kawo komai sai halaka.
11. Ka Da Ka Biye Sha’awa:
Zina, madigo da luwadi suna kawo asara a duniya da lahira. Mutum mai tsoron Allah baya biye wa zuciya.
---
Wannan nasiha ce ga mai so a girmama shi, a daraja shi, kuma a ɗauke shi da kima.
Ka kiyaye ka tsira.
Comments