Internet na nufin wani babbar hanyar sadarwa ce da ke haɗa kwamfutoci da na’urori daga sassa daban-daban na duniya, ta hanyar musayar bayanai da saƙonni. Ana iya amfani da internet wajen:
Bincike da karatu: Google, Wikipedia da sauran shafuka.
Sadarwa: Email, WhatsApp, Facebook, da sauransu.
Kasuwanci: Siyar da kaya ko ayyuka ta yanar gizo.
Kallo da saurare: YouTube, Netflix, da sauransu.
Yana taka muhimmiyar rawa a rayuwa ta yau da kullum, musamman a fannin ilimi, sadarwa, kasuwanci, da nishaɗi.
Comments