KASHI NA ƊAYA: RANAR DA TA CANZA KOMAI
A cikin ƙauyen Dandume, wani matashi mai suna Sulaiman yana zaune da mahaifiyarsa mai suna Inna Hauwa'u. Rayuwarsu cike take da ƙalubale, amma suna zaune cikin ƙauna da dogaro da Allah. Mahaifin Sulaiman ya rasu tun yana ƙarami, hakan yasa Sulaiman ya ɗauki nauyin kula da mahaifiyarsa tun yana ɗan shekara goma sha biyar.
Kullum da safe, Sulaiman yana tashi ya tafi gona, yana bin gonakin mutane yana yin aiki don samun abinci da ƙaramar kuɗi don kula da mahaifiyarsa. Duk da ƙuncin rayuwa, bai taɓa korafi ba.
Amma wata rana, bayan dawowarsa daga aiki, ya samu Inna Hauwa’u a kwance – tana ta rawar sanyi, idonta cike da hawaye, kuma jikinta na karkarwa. Ya ruɗe, ya ɗauki guntun kuɗin da ya tara domin siyan abinci, ya nufi asibitin garin.
Kuma wannan rana ce ta fara canza rayuwarsa gaba ɗaya...
Comments