SABON TSARIN DA COMPANY AIRTEL SUKA GABATAR A YAU
MUHIMMIYAR SANARWA ZUWA GA DUK WANI MA'AIKACINSU:
❗❗❗
A yayinda Company Airtel suka dawo da yin rijistar sabbin layukan waya (sim) bayan fama da gyararraki da suka gabatar a wannan hanyar sadarwa, suna sanar da ku cewa ba a yarda da rashin bin ƙa'ida da zamba a cikin harkar kasuwanci. Wannan kamfani ba zai lamunci ko ɗaya daga ciki ba.
---
❗ Me ake nufi da rashin bin ƙa'ida (non-compliance) da zamba (fraud)?
1. Kada ka kunna (activate) layin waya a wajen yankin da aka kulle maka (geolocked location).
(Wato ka yi aiki ne kawai a yankin da aka ba ka izini).
2. Kada ka yi amfani da NIN ɗin abokin ciniki don kunna layi fiye da ɗaya lokaci guda.
3. Kada ka kunna layuka da yawa da nufin sayar da su a matsayin waɗanda aka riga aka yi musu rajista (pre-registered sims).
4. Kada ka ba wani lambar shiga (login ID) naka, ko kuma ka ba wani kayan aiki naka (kit) ya yi aikin madadinka.
5. Kada ka yi amfani da NIN ɗin wani don yin rajista ba tare da yardarsa ba.
6. Kada ka yi SIM swap (canjin layi) da wata hanya da ba ta da gaskiya.
(Idan baka tabbatar da cewa wanda ke buƙatar SIM swap ɗin shi ne sahihi ba, kada ka yi masa. A tura shi ofishin Airtel.)
7. Kada ka yi rajistar wanda bai kai shekaru 18 ba.
8. Kada ka yi ƙoƙarin kaucewa yin amfani da hanyar tantance biometric da aka sa don tabbatar da kai ne wakili.
---
🚫 Me ake nufi da "Zero Tolerance"?
> Wato idan har ka karya wata daga cikin waɗannan dokoki sau ɗaya kawai, za a dauki mataki ba tare da ba ka damar gyara ba.
Za a rushe yarjejeniyar aiki da kai a matsayin wakili na Airtel KYC.
Za a toshe lambar da kake amfani da ita (MSISDN) da kuma NIN ɗinka daga tsarin.
Za a mika bayananka ga hukumomin tsaro don ci gaba da bincike ko ɗaukar matakin shari’a.
---
🗣️ Manajojin ku (ASM da MD) za su ci gaba da bayyana muhimmancin bin ƙa’ida da bin dokokin hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC).

Comments