Ga sirrikan kamar haka:
Wayar Android na dauke da wasu sirruka masu ban mamaki da mutane da dama basu sani ba.
Ga muhimman fasaloli guda 5 da zasu taimaka maka amfani da wayarka cikin hikima:
---
1. Screen Pinning – Kulle App ɗaya kawai
Wannan fasalin yana ba ka damar kulle wayarka a cikin app ɗaya. Idan ka ba wani wayarka, ba zai iya fita daga wannan app ba har sai an buɗe ta.
Amfani: Idan kana ba yara ko abokai wayarka, ba za su iya shiga sauran apps ba.
Yadda ake kunna shi:
Je zuwa Settings > Security (ko Security & Location)
Nemi Screen Pinning, sai ka kunna shi
Danna Recent Apps, sai ka danna icon ɗin app ɗin da kake so ka yi pin
Danna 📌 Pin — Shikenan!
---
2. Smart Lock – Buɗa Wayarka A Wurin da Ka Yarda da Shi
Smart Lock yana baka damar barin wayarka a buɗe idan tana wurin da ka amince da shi (misali: gida ko mota), ko tana haɗe da wata na’ura kamar smartwatch.
Amfani: Ba sai ka dinga saka password ko fingerprint kullum ba.
Yadda ake kunna shi:
Je zuwa Settings > Security > Smart Lock
---
3. Split Screen Mode – Aiki da Apps 2 lokaci guda
Za ka iya raba allo ka yi amfani da apps biyu lokaci ɗaya, misali: kallon YouTube da hira a WhatsApp.
Yadda ake yi:
Danna Recent Apps
Danna icon ɗin app ɗin
Zaɓi Split Screen
Zaɓi app na biyu — Shikenan!
---
4. Screen Recorder – Yin Bidiyon Abinda ke Kan Allo
Wasu wayoyin Android na zuwa da Screen Recorder built-in, ba sai ka sauke wata app ba.
Yadda ake amfani da shi:
Je zuwa notification panel
Nemi Screen Recorder icon, sai ka danna shi
Za ka iya zaɓar yin recording tare da sauti.
---
5. Live Caption – Fassarar Sauti Zuwa Rubutu
Wannan fasalin yana canza duk wani sauti daga video ko audio zuwa rubutu kai tsaye, ko da babu internet.
Amfani: Yana taimaka wa kurame ko lokacin da kake a wuri mai buƙatar shiru.
Yadda ake amfani da shi:
Je zuwa Settings > Accessibility > Live Caption
Ka kunna Use Live Caption
Ko kuma danna Volume Up + Down lokaci guda, sai ka ga icon ɗin (CC), ka kunna shi.
Comments