🏛️ Menene SCUML? SCUML (Special Control Unit Against Money Laundering) wata ƙungiya ce karkashin EFCC a Najeriya, wadda aka kafa bisa sashe na ƙasa Money Laundering (Prevention and Prohibition) Act 2022. Alhakin su shi ne saka ido kan kamfanoni, ƙungiyoyi da wasu masana’antu domin tabbatar da cewa ba a amfani da su wajen wanke kuɗi ko laifukan kuɗi. --- ✅ Me Kake Bukata Don Yin Rijistar SCUML? 📄 Takardun da ake buƙata: Ga kamfanonin Limited Liability (LLC): Certificate of Incorporation (CAC) Memorandum & Articles of Association (MEMART) Status Report (CAC 1.1 ko CAC 7 & CAC 2) Tax Identification Number (TIN) printout BVN + bank name da account number na daraktocin kamfani Letterhead na kamfani Valid ID na ɗaya daga cikin daraktoci Takardun ƙwarewa (idan sana’a ce ta ƙwararru) Ga ‘Business Name’ (Proprietorship): Certificate na rajistar kasuwanci (BN-01) Form BN-01 (bayanan mallakin) TIN printout BVN + bank account details Ga NGOs / NPOs: Certificate of Incorporati...
KANA SO ƊAN ADAM YA DINGA GANIN DARAJARKA? 1. Ka Rage Magana: Yawan magana ba alamar wayo ba ce. Halittar ɗan Adam ta zo da kunne biyu da baki ɗaya – domin a fi sauraro fiye da magana. 2. Ka Koyi Faɗin "A'a": Kar ka dinga amincewa da abubuwan da zasu cutar da kai kawai don ka faranta. Alkawarin da ya fi ƙarfin ka yana kawo saɓani da raini. 3. Kada Ka Yiwa Tambaya Amsa Da Gaggawa: Idan aka tambaye ka, kayi shiru ɗan lokaci – kayi tunani kafin ka bada amsa. Maganar da ta fita ba zata dawo ba. 4. Yi Tunani Kafin Yanke Hukunci: Gaggawa aikin shaidan ne. Wanda ya yi garaje yafi saurin tuntuɓe da nadama. 5. Ka Rage Yawan Nunawa Kanka: Kar kowa ya dinga ganinka sai dai a wuraren da suka dace kamar wajen aiki. Abinda yafi yawa yana rasa kima. Daraja na buƙatar sirri da natsuwa. 6. Ka Guji Gardama Da Kowa: Musamman da abokai ko iyali. Yawan gardama yana nuna ƙarancin hankali da rainin wayo. Yana iya kawo kiyayya da rashin daraja. 7. Kullum Ka Saka Tufafin Tsabta: Ko da...